Isa ga babban shafi
Burundi

Burundi ta daure Sojojin da suka jagoranci juyin mulki

Kotun koli a Burundi ta zartar da hukuncin daurin rai da rai akan wasu manyan hafsoshin sojin kasar da suka jagoranci juyin mulkin da aka murkushe a kasar.

Sojojin da kotu ta daure a Burundi
Sojojin da kotu ta daure a Burundi REUTERS
Talla

Janar Godefroid Nyombare, wanda ya jagoranci juyin mulkin domin hambarar da gwamnatin Pierre Nkurunruziza yana cikin wadanda kotun ta daure rai da rai duk ya tsere baya cikin kasar.

Sannan akwai wasu manyan hafsan soja guda hudu da suka hada tsohon ministan tsaro Cyrille Ndayirukiye da Zenon Ndabaneze da Juvenal Niyungeko da kuma janar na ‘Yan sanda Hermenegilde Nimeny da kotun ta daure.

Baya ga laifin juyin mulkin, kotun kuma ta kama su da laifin kisan Sojoji da ‘Yan sanda da fararen hula tare da lalata gidajen jama’a.

Akwai kuma wasu jami’an tsaro da suka hada da ‘Yan sanda da Sojoji da kotun ta daure shekaru 30 wadanda suka taimaka wajen juyin mulkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.