Isa ga babban shafi
Burundi

AU za ta sanya takunkumi a Burundi

Kungiyar tarayyar Afrika, AU ta yi barazanar sanya takunkumi kan bangarorin da ke yaki da juna a Burundi matukar suka ki halartar zaman tattaunawar sulhu da za a gudanar a watan gobe a Tanzania, yayin da ta bukaci gwamnatin kasar da ta karbi dakarun wanzar da zaman lafiya.

Shugabar hukumar tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini-Zuma.
Shugabar hukumar tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini-Zuma. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

A ranar litinin ce tawagar gwamnatin Buruni da ta ‘yan tawayen kasar suka gana a Uganda kuma ana sa ran za su sake zama a ranar 6 ga watan Janairun sheara mai kamawa a birnin Arusha na Tanzania domin tattaunawa kan yadda za a kawo karshen rikicin kasar.

To sai dai tawagar gwamnatin Burundi ta ce, babu wata yarjejeniya da aka cimma dangane da hakikanin ranar da za a sake zaman.

Tuni dai shugabar hukumar tarayyar Afrika, Nkosazana Dlamini-Zuma ta gargadi sanya takunkumi ga bangarorin biyu matukar suka katse tattaunawar sulhu a tsakaninisu tare ci gaba da fafatawa da juna.

A bangare guda, kungiyar AU ta bukaci Burundi da ta karbi dakarun wanzar da zaman lafiya 5,000 amma gwamnatin kasar ta nuna adawarta da matakin kuma shugaba Nkrunziza ya ce zai sa kafar wando daya da dakarun na AU da ake sa ran za su kare lafiyar fararan hula a Burundi.

Tun a watan Aprilun da ya gabata, kasar ta fada cikin wani hali bayan shugaba Nkurunziza ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takara domin neman wa’adi na uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.