Isa ga babban shafi
Burundi

Amurka ta bukaci ‘Yan kasarta su fice Burundi

Gwamnatin kasar Amurka ta umurci ‘Yan kasarta su gaggauta ficewa Burundi saboda rikicin kasar da ke ci gaba da kazancewa.Wannan na zuwa ne bayan mutuwar mutane 90 a rikicin da ya faru a ranar Juma’a a Bujumbura.

Ana zaman dar dar a Burundi
Ana zaman dar dar a Burundi REUTERS/Jean Pierre Aime Harerimana
Talla

Mai Magana da yawun sojan kasar Gaspard Baratuza ya fadi cewa wasu ‘yan bindiga ne suka kai hari a wurare uku na barikicin Sojoji, inda aka kashe 79 tare da kame wasu 45.

Kisan shi ne mafi muni tun bayan da shugaban kasar Pierre Nkuruziza ya zarce da mulkin kasar wa’adi na uku da karfin tsiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.