Isa ga babban shafi
Burundi

MDD ta la’anci harin Burundi

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi allawaddai da munanan hare haren da ‘yan bindiaga suka kai a barikin Sojoji a Burundi a safiyar Juma’a, tare da yin kiran bin hanyoyin tattaunawa domin tabbatar da zaman lafiya a kasar da ke fama da rikici.

Dubban Mutanen Burundi suka tsere zuwa Rwanda saboda rikici
Dubban Mutanen Burundi suka tsere zuwa Rwanda saboda rikici REUTERS/Goran Tomasevic/Files
Talla

Rundunar Sojin Burundi tace an yi nasarar kashe mahara 12 tare da kame wasu 21 wadanda suka kaddamar da hari da sanyin safiya a barikin Sojoji a Bujumbura.

Jekadiyar Amurka Samantha Power da ke magana da yawun mambobgin kwamitin tsaro 15 ta yi kira dukkanin bangarorin Burundi su kaucewa rikici.

Burundi dai ta fada rikici tun lokacin da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya bayyana kudirin zarcewa kan madafan iko karo na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.