Isa ga babban shafi

‘Yan bindiga sun raunana wani kwamandan Sojin Burundi

Wasu ‘Yan bindiga sun raunana wani daga cikin manyan kwamandojin Sojin kasar Burundi a wani harin kwantar bauna da suka ma shi a Bujumbura. ‘Yan bindigar sun harbi Kanar Serges Kabanyura a ranar Lahadi lokacin ya ke kan hanya cikin motarsa a Bujumbura.

Burundi ta fada cikin rikici tun lokacin da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya bayyana matakin neman wa'adin shugabanci na uku
Burundi ta fada cikin rikici tun lokacin da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya bayyana matakin neman wa'adin shugabanci na uku AFP PHOTO / SIMON MAINA
Talla

Wani Soja da ke cikin tawagar Kanar din, ya shaidawa manema labarai cewar suna kan hanyar su ne zuwa Bujumbura daga Yankin da kwamandan ke aiki ‘yan bundigan suka bude musu wuta, suka raunana biyar daga cikinsu.

Wannan na zuwa bayan harin da ‘Yan bindiga suka kai a ranar Juma’a inda suka harbi daya daga cikin ‘yan majalisun kasar daga jam’iya mai mulki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.