Isa ga babban shafi
Chad

Ta’addanci ya fi Ebola illa- Deby

Shugaban Kasar Chadi Idris Deby ya ce illar ayyukan ta’addanci ya zarce barnar da cutar ebola ke yi, saboda yawan mutanen da ke salwanta a hare haren ta’addanci da ake fakewa da addini.

Shugaban Chadi Idriss Deby
Shugaban Chadi Idriss Deby Photo AFP / Bertrand Guay
Talla

Shugaban ya fadi haka ne a lokacin ya ke jawabi a Ouagadougou a ziyarar jaje da ya kai Burkina Faso kan harin ta’addancin da ya hallaka rayukan mutane 30.

Shugaban ya ce ba zasu lamunce da yadda mahaukata ke kashe mutane ba-ji-ba-gani ba.

Sannan Shugaban na Chadi ya bukaci kiran wani taro na musamman na kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Nijar a Addis Ababa hedikwatar kungiyar kasashen Afirka a ranar 31 ga wata don tattauna halin da kasashe ke ciki.

Kasar Chadi na daya daga cikin kasashen da ke fama da hare haren kungiyar Boko Haram na Najeriya da suka addabi Nijar da Kamaru.

Yanzu haka kuma mayakan al Qaeda reshen Maghrib na barazana ne ga kasashen Mali da Mauritania da Burkina Faso

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.