Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Mutane 29 sun mutu a harin da al-Qaeda ta kai Burkina Faso

Akalla mutane 29 ne suka mutu, akasarin su ‘yan kasashen ketere, a wani mummunan harin da kungiyar al-Qaeda a yankin Magreb ta kaddamar kan wani Otel da ke babban birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso.

An kubutar da mutane 176 bayan jami'an tsaro sun karbe iko da Otel din mai suna Four-Star Splendid
An kubutar da mutane 176 bayan jami'an tsaro sun karbe iko da Otel din mai suna Four-Star Splendid REUTERS/Joe Penney
Talla

Cikin wadanda aka hallaka akwai ‘yan kasar Canada 6 da Farasansawa guda biyu da ‘yan kasar Switzerland biyu har ma da Ba’amurke guda.

Ministan cikin gidan kasar, Simon Campaore ya bayyana cewa an kubutar da mutane 176 bayan jami’an tsaro sun karbe iko da Otel din mai suna Four-Star Splendid a jiya Asabar.

An dai shafe fiye sa’oi 12 ana gugurzu kafin daga bisani jami’an tsaron su karbe iko da Otel din kuma sama da mutane 50 aka rawaito cewa sun jikkata sanadiyar harin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.