Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Pistorius zai fuskanci hukunci shekaru 15 a gidan yari

Kotun daukaka karar ta Afrika ta kudu ta samu fittacen dan tseren nakasasu kasar Oscar Pistorius, da laifin kisan budurwarsa Reeva Steenkamp, tare da yanke masa hukunci zaman gidan yari na tsawon shekaru 15.

Fittacen dan wasan tseren Nakasasu Oscar Pistorius
Fittacen dan wasan tseren Nakasasu Oscar Pistorius REUTERS/Herman Verwey/Pool
Talla

Alkalin Kotun ya yanke wannan hukunci ne bayan ya yi watsi da hukuncin da wata kotun daukaka karar ta kasar ta yanke a baya, cewa Pisotorious ya aikata kisan ne ba da gangan ba.

Oscar Pistorious ya harbe Budurwarsa ne da bindiga har sau 4 a lokacin da take makewaye, sai dai ya ce ya aikata haka ne bayan y ayi zatan kutse akayi masa a gida.

A cikin watan Oktober aka koma yiwa Pistorious daurin talala bayan ya kwashe shekara 1 cikin 5 da aka yanke masa a gidan kaso.

Sai dai a wannan lokaci alkali Eric Leach ya yi watsi da duk wani bayanai na Oscar tare da kama shi da laifin kisa, inda a yanzu zai fuskanci hukunci dauri da ka iya kaiwa tsawon shekaru 15 a gidan kaso.

Mai shigar da karar a kasar ya ce a yanzu, Oscar mai shekaru 29 zai cigaba da kasancewa a daurin talala na dan wani dan loakci, kafin daga bisani ya sake komawa kotun domun fuskantar wannan hukunci.

Tuni dai Iyayyen Reeva suka nuna gamsuwarsa da wannan hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.