Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Kotu ta samu Pistorius da alhakin mutuwar Budurwar shi

Kotun Birnin Pretoria ta samu Dan tseren guragu, Oscar Pistorius da alhakin kisan budurwar shi Reeva Steenkamp a gidanshi, laifin da kuma zai sa kotu ta yanke masa hukunci dauri a gidan Yari. Tuni Mai shari’ar da ke sauraren Karar Oscar Pistorius tace ta gano Dan tseren gudun guragun ba da gangan ba ne ya kashe Budurwarsa, bayan shafe lokaci mai tsawo ana tabka shari’a a Afrika ta Kudu.

Oscar Pistorius, dan tseren gudun guragu da ake tuhuma ya bindige Budurwarsa a Afrika ta kudu
Oscar Pistorius, dan tseren gudun guragu da ake tuhuma ya bindige Budurwarsa a Afrika ta kudu REUTERS/Phill Magakoe
Talla

A ranar masoya da ake kira Valentine ne a bara, Pistorius ya harbe budurwarsa da bindiga a gidansa.

Kuma Pistorius ya amsa laifin bindige Reeva amma kuma ya musanta aikata harbin da gangan, yana mai cewa ya yi harbi ne akan tunanin wani ne ya kutsa ma sa a cikin gida.

Mai Shari’a Masipa tace cikin sakaci Pistorius ya harba bindiga, tana mai cewa duk wani mai tunani zai yi kokarin kaucewa abin da ya faru.

Nan da makwanni masu zuwa ake sa ran Kotu zata yanke wa Pistorius hukunci bayan kama shi da laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.