Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Kotu ta ba da belin dan tseren nakasassu Oscar Pistorius

A dazun nan, wata kotun majistare a Africa ta kudu, ta bayar da belin shahararren dan tseren nakasassun kasar, Oscar Pistorius, yayin da a ranar 4 ga watan Yuni, za a ci gaba da shari’a kan zargin da ake mishi, na hallaka budurwar shi, Reeva Steenkamp. 

Oscar Pistorius
Oscar Pistorius REUTERS/Dylan Martinez
Talla

Bayan da aka shafe kwanaki 4 a fadi tashin shari’a da ya daga hankulan ‘yan kasar, yanzu dai mai shari’a Desmond Nair, yace yana da yakinin Pistorius ba zai gudu ba, kuma ba zai zama barazana ga jama’a ba.

Yayin da alkalin ke magana, dan wasan mai shekaru 26 ya tsaya yana saurare cikin kwalla, inda mai shari’a yace, ba batun ko yana da laifi ko a’a ba ne, sai dai abu ne da ya shafi shari’a.

Pistorius ya ki amsa lafin kisan da ya yiwa budurwar ta sa, Reeva Stenkamp, ‘yar shekaru 29 wacce kuma ya hadu da ita a watannin baya-bayan nan.

Shugaban shigar da karar a gaba kotu, Garriel Nel ya nemi da kada kotun ta bada belin Pistorius domin a cewarsa har yanzu bai fahimci girman laifin da shi Pistorius ya yi ba.

A ranar 14 ga watan Febrairu ne, Pistorious ya harbe Steenkamp a gidansa bayan ya yi zaton wani ne ya shiga gidansa ba tare da saninsa, inda kuma ta mutu nan take.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.