Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Pistorius yace ba da son ran shi ba ne ya bindige budurwar shi

Dan tseren gudun Nakkassu Oscar Pistorius yace ba da son ranshi bane ya bindige budurwar shi a lokacin sauraren karar shi a Kotun Afrika ta Kudu. Wannan ne batu na farko da ya fito daga bakin dan wasan tun bayan mutuwar budurwar shi Reeva Steenkamp a ranar 14 ga watan Fabrairu.

Oscar Pistorius a kotun Pretória
Oscar Pistorius a kotun Pretória REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Mai gabatar da kara a kotun Desmond Nair, yace ba zai bayar da belin Dan wasan ba sannan za’a iya kama shi da laifin kisa.

Oscar Pistorius ya amsa yin harbi a gidansa tare da yin ihu bayan harba hasashi.

Kamfanonin Amurka guda biyu Nike da Oakly da ke daukar nauyin Oscar Pistorius, sun katse hulda da shi saboda tuhumar da ya ke fuskanta akan ya kashe budurwar shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.