Isa ga babban shafi
Ebola

Ebola: Ana sa ido kan mutane 153 a Liberia

Hukumomin Kasar Liberia na sa ido kan mutane 153 da suka yi mu’amala da wasu mutane 3 da ke dauke da cutar Ebola da ta sake bulla a kasar.

Ebola ta dawo a Liberia bayan ta kashe mutane sama da 4000
Ebola ta dawo a Liberia bayan ta kashe mutane sama da 4000 Daniel Berehulak pour le New York Times / Getty Images
Talla

Rahotanni sun ce an samu mutane 3 da suka kamu da cutar ranar juma’a, wadanda suka hada da wani yaro mai shekaru 15 da ake kira Nathan Gbotoe a wajen birnin Monrovia, wanda tuni aka tabbatar da cewar mutanen gidan su biyu sun harbu da cutar

Babban jami’in lafiyar kasar Dr Francis Kateh, ya tabbatar da cewar mutane 3 sun kamu da cutar, kuma suna sa ido kan mutane 153 da suka yi mu’amala da su yanzu haka.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi kira ga mutanen kasar su kwantar da hankalinsu domin jami’anta na kan aikin kawar da cutar.

A watan Satumba ne aka bayyana kawo karshen cutar Ebola a Liberia bayan cutar ta kashe mutane sama da 4,000 a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.