Saliyo
Saliyo ta rabu da cutar ebola
Ranar Asabar mai zuwa ne ake saran ayyana kasar Saliyo a matsayin wadda ta rabu da cutar ebola bayan an kwashe kwanaki 42 ba tare da samun wanda ya kamu da cutar ba.
Wallafawa ranar:
Talla
Sai dai har yanzu al’ummar kasar wadda ta rasa mutane sama 4,000 na ci gaba da zaman dar dar ganin yadda cutar ke ci gaba da hallaka mutane a kasar Guinea da ke makwabtaka da ita.
Palo Conteh, shugaban kai dauki kan masu fama da cutar a Saliyo ya ce babu wani biki da za a yi ranar a Asabar, sai dai kawai farin cikin cewar sun rabu da cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu