Isa ga babban shafi
Saliyo

An kawo karshen killace mutane 500 a Saliyo saboda Ebola

Kasar saliyo ta kawo karshen killace mutane 500 bayan shafe kwanaki 21 na gudanar da bincike ko suna dauke da cutar Ebola a kauyen Massessbe dake Arewacin Kasar. 

Jami'an dake yaki da Ebola a Saliyo
Jami'an dake yaki da Ebola a Saliyo Reuters/Josephus Olu-Mammah
Talla

Shugaban Kasar Ernest Bai Koroma ya ce, mutane biyu ne kacal a yanzu ke fama da cutar a duk fadin Kasar, kuma suna ci gaba da samun kulawa.

Ministan lafiya ya tabbatarwa kamfanin dillacin labaran faransa cewa, babu wani daga kauyen da aka samu dauke da cutar ko kuma alamarta.

To sai dai duk da haka, shugaba Koroma ya gargadi cewa kada a yi sake wajen kawar da cutar baki daya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.