Isa ga babban shafi
China-Liberia

China za ta gina wa Liberia sabuwar hanya kyauta

Kasar China ta yi alkawarin ginawa kasar Liberia hanyar mota ta zamani kyauta, a matsayin nata gudunmawa ga kasar da ke farfadowa daga annobar cutar Ebola.

Cutar Ebola ta kashe mutane da dama a Liberia
Cutar Ebola ta kashe mutane da dama a Liberia AFP PHOTO / DOMINIQUE FAGET
Talla

Ministan waje na kasar China Wang Yi wanda ya ke rangadi a kasar Liberia ya shaidawa taron manema labarai a Monrovia cewa China zata yi amfani da kudadenta da ta ware domin Afrika wajen wannan aiki.

Ya fadi cewa kasar China har ila yau, zata gina rukunin ofisoshi na ma’aikatu 10.

Wannan hanya da kasar China za ta samar zai kasance dab da gaban ruwan kasar Liberia ne inda ake gudanar da harkokin kasuwanci.

Ministan wajen na kasar China wanda ya ke rangadin kasashen Liberia da Guinea da Saliyo wadanda suka yi fama da annobar cutar Ebola, ya ce China na shirye domin kulla zumunci mai karfi da kasar Liberia, ta yadda harkan kasuwanci zai kankama tsakaninsu.

Tun bullar cutar Ebola a shekara ta 2013 cutar ta kashe mutane 4,800 a Liberia, yayin da a kasashe uku na yankin cutar ta kashe mutane 11,300, amma kuma ya zuwa yanzu cutar ta ragu matuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.