Isa ga babban shafi
Liberia

An sallami majinyatan Ebola a Liberia

Jami’an kiwon lafiya sun sallami mutane hudu na karshe da ke jinyar cutar Ebola a birnin Monrovia na kasar Liberia, lamarin da ke tabbatar da cewa a yanzu ba wani da ke fama da cutar a duk fadin kasar.

Jami'an lafiya da ke yaki da Ebola a Liberia
Jami'an lafiya da ke yaki da Ebola a Liberia RFI
Talla

Mahukuntan lafiya a Liberia sun ce sun sallami wasu mutane biyu da yara guda biyu da ake kula da lafiyarsu a asibitin Monrovia bayan sun samu sauki.

A ranar 9 ga watan Mayu ne aka bayyana cewa an kawo karshen annobar Ebola a kasar, amma daga baya sai wani matashi mai shekaru 17 ya rasu sakamakon harbuwa da ita, lamarin da ya sa aka ci gaba da binciken aikin yaki da ita a sauran sassan kasar.

Ebola ta kashe mutane da dama a Liberia da Saliyo da kuma Guinea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.