Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya-Congo

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo na shirin janye dakarun ta daga Africa ta Tsakiya

Hukumomi a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo na shirin janye illahirin sojojin kasar da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sakamakon zargin aikata lalata da mata a kasar.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Congo Demokradiyya
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Congo Demokradiyya RFI
Talla

A jimilce dai sojoji 400 ne daga jamhuriyar ta Congo ke aiki a karkashin rundunar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta Minusca a jamhuriyar Afrika ta tsakiya,
bayanai na nuni da cewa za a janye dakarun ne domin gudanar da bincike akan wannan zargi da ake yi masu.

Matakin janye dakarun ya biyo bayan wani taro ne da kwamitin tsaro na Majalisar Dimkin Duniya ya yi inda a lokacin ya yanke shawarar kin sabunta wa’adin aikin sojojin na Congo a kasar.

Ana dai zargin dakarun na Congo ne da aikata fyade akan mata da ke cikin sansanonin ‘yan gudun hijira a yankin Bambari, lamarin da ya shafi kimar ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.