Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Kerry ya ce bai kamata Kabila ya sake tsayawa takarar a 2016

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce dole ne shugaban Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo Josheph Kabila ya mutunta kundin tsarin mulkin kasar, ta hanyar kaucewa sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2016.

John Kerry da Joseph Kabila a birnin Kinshasa.
John Kerry da Joseph Kabila a birnin Kinshasa. REUTERS/Saul Loeb/Pool
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka wanda ke gudanar da ziyarar aiki a birnin Kinshasa, ya shawarci shugaba Kabila da ya kaucewa canza kundin tsarin mulkin kasar, kafin daga bisani ya bayar da sanarwar cewa Amurka za ta bai wa kasar tallafin dala milyan 30 domin shiryawa zaben mai zuwa.

Yanzu haka dai da dama daga cikin masu adawa da gwamnatin kasar ta Congo na ci gaba da fafutukar ganin cewa shugaba Kabila bai sake tsayawa takara a zaben na shekara ta 2016, yayin da wasu majiyoyi ke cewa shugaban na da niyyar canza kundin tsarin mulkin kasar domin sake tsayawa takarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.