An an fadada dokar haramta amfani da hijabi a kasar Kamaru
Mahukuntan kasar Kamaru sun sake fadada dokar haramta amfani da hijabi ko burqa, a kokarin da suke yi na kawar da ‘yan kungiyar Boko Haram, dake ci gaba da kai hare haren kunar bakin wake a yankunan kasar.
Wallafawa ranar:
Wannan matakin na zuwa ne kasa da wata daya, bayan da wasu mata ‘yan kunar bakin wake, sanye da hijabin, suka tayar da bama bamai a wani yankin dake kan iyakar kasar da Nigeria, daga arewaci, inda suka hallaka mutane 11.
Gwamnan Lardin Gabas daya jagoranci taron kwamitin tsaron yankin, da ya sami halartar manyan malaman addin Isalama, ya bi sawun takwarorisa na Arerwaci da Yammacin kasar, na haramta sanya hijabin.
Mai magana da yawun gwamnatin lardin yammacin kasar, yankin da birnin Douala yake Mireille Bisseck, yace daga yanzu an hana dinkawa, da sanya hijabin a kasar.
Bisseck ya kuma ce za a kara sa ido kan kiran sallah da ake yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu