Isa ga babban shafi
Birtaniya-Media-Islam

An fara muhawarar haramta sanya hijabi a Birtaniya

An fara muhawarar haramta sanya hijabi a kasar Birtaniya a baina jama’a inda ‘yan siyasa da wata babbar jaridar kasar ke kira da a bi sahun sauran kasashen Nahiyar Turai da suka harmta sanya hijabin.

Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron
Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron REUTERS/UK Parliament via Reuters TV
Talla

Batun ya kunno kai ne bayan wata kotun kasar ta bawa wata mata iznin bayyana a gaban kotun sanye da cikakken hijabi amma tare da yaddar cewa za ta cire idan za ta ba da shaida.

Jaridar The Sun wacce sayar da guda miliyan 2.25 ta buga hoton matar a lokacin da ta bayyana a kotu tana mai kira da a yi dubi akan batun.

Kasar Birtaniya dai bat a cikin kasashen da suka haramta sanya hijabi a baina jama’a, inda akan samu mata da dama suna saka shi, musamman ma a birane irinsu London da Birmingham da kuma Bradford.

Batun saka hijabi a Birtaniya wani lamari ne da kasar ke kaucewa tun a da musamman saboda ikrarin da kasar ke yi na kasancewa mai zaman tsaka-tsaki akan batutuwan da suka shafi addini.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.