Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Birtaniya ta gabatar da kudirin abka wa Syria

Kasashen Biyar masu kujerun dindindin a Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da tattaunawa kan wani daftari da Birtaniya ta gabatar da ke neman a bai wa kasashen duniya damar kai wa kasar Syria harin soja.

Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron
Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron REUTERS/Stefan Wermuth
Talla

Rahotanni sun ce ana gudanar da tattaunawar ne a asirce, domin samun amincewa ko akasin haka akan kudurin da Birtaniya ta ce ta gabatar da shi ne domin bayar da kariya ga fararen hula a kasar Syria.

Sai dai har yanzu kasashen Yamma musamman ma Amurka da Birtaniya da kuma Faransa, na ci gaba da fuskantar turjiya daga kasar Rasha dangane da wannan batu.
Sakataren Majalisar, Ban Ki-moon ya nemi bangarorin su nemo hanyoyin sansanta banbancin da ke tsakaninsu domin daukar mataki na bai daya.

Yanzu haka dai akwai wakilan Majalisar Dinkin Duniya da ke ci gaba da gudanar da bincike a yankunan da aka ruwaito an kai hare haren makamai masu guba a cikin kasar Syria.

Ban Ki-moon yace wakilan suna bukatar kwanaki hudu domin kammala aikin bincikensu, yana mai kira ga kwamitin tsaro ya jinkirta daukar mataki har sai an kammala gudanar da binciken.

Kasashen Amurka da aminanta suna zargin Dakarun Assad ne da kai hare haren yayin da Gwamnatin Syria ta musanta zargin tana mai ikirarin ‘Yan tawaye ne suka kai hare haren.

Kasar Rasha tace kwamitin yana kokarin yin gaggawar abkawa Syria ne ba tare tantance gaskiyar al’amarin ba.

Irin haka ne ta faru da Libya inda Amurka da Birtaniya da Faransa suka taimakawa ‘Yan tawaye kawo karshen Kanal Ghaddafi wanda ya kwashe shekaru sama da 40 yana shugabanci

Yanzu haka dai Amurka ta fara tuntubar kasashen Larabawa da suka hada da Turkiya da Jordan da sauran aminanta domin shirya kai wa Assad hari.

Kuma sakataren Tsaron kasar Chuck Hagel yace Amurka har ta kammala kimtsawa domin kaddamar da yaki a Syria, illa suna jiran umurni ne daga Obama.

Kasar Rasha ta yi gargadin abinda zai iya biyo wa baya idan har aka dauki matakin abkawa Syria.

Gwamnatin Syria tace manyan kasashen na Yammaci suna neman hanyoyi ne domin kawo karshen Assad.

A watan Maris din shekarar 2011 ne al’ummar kasar Syria suka kaddamar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar al Assad, lamarin da ya rikide ya koma yakin basasa.

Alkalumman Majalisar Dinkin Duniya sun ce sama da mutane 100,000 ne suka mutu kuma dubban mutane ne suka fice Syria domin tsira da ransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.