Isa ga babban shafi
Amurka-Syria-Rasha

Amurka tana tunanin daukar mataki akan Assad na Syria

Amurka ta ce kasar Syria na iya fuskantar mummunan martani daga kasashen duniya sakamakon yin amfani da makamai masu gubu a kan jama’a, a yayin da jami’an Majalisar Dinkin Duniya ke ci gaba da gudanar da bincike amma kasar Rasha tace har yanzu babu gaskiyar zargin da ake wa Assad.

Shugaban Amurka Barack Obama, yana ganawa da Vladimir Putin na Rasha
Shugaban Amurka Barack Obama, yana ganawa da Vladimir Putin na Rasha REUTERS/Jason Reed/Files
Talla

Wata alama da ke kara tabbatar da sabanin da ke akwai tsakanin Amurka da Rasha dangane da batun na kasar Syria, kasashen biyu sun soke tattaunawar da ya kamata su yi a cikin wannan mako domin samar da hanyoyi na diflomasiya da nufin warware rikicin.

Rahotanni sun ce Amurka da aminanta suna shirin yin taron dangi akan Bashar al Assad na Syria sakamakon yin amfani da makamai masu guba, Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry yace Assad yana rufa rufa ne.

Kasar Rasha ta yi gargadin hatsarin da za’a samu idan har aka abkawa Syria, tana mai jaddada cewa kaddamar da yaki a kasar ba tare da tabbatar da amfani da makamai masu guba ba sun sabawa dokokin duniya.

A nata bangaren kasar Faransa, wadda ke da kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ta tura ministanta na harkokin waje zuwa kasashen Larabwa domin tattaunawa akan batun Syria.

Rikicin Syria dai ya raba kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya gida biyu inda Rasha da China ke hawa kujerar na-ki ga duk wani kudiri da sauran mambobin kwamitin ke kokarin dauka akan Assad.

A shekarun baya Amurka ta shiga yakin Kosovo ba tare da amincewar Kwamitin Sulhu ba a 1999 kuma yanzu tana shirin shiga Syria.

Akwai kuma wasu manyan kasashen Larabawa da ke shirin hada hannu da Amurka da aminanta Faransa da Birtaniya domin abkawa Bashar Assad na Syria.

Masana suna ganin yadda wasu kasashen Larabawa suka mara wa Amurka baya a yakin Libya a 2011, babu tantanma za su sake bayar da goyon bayansu a yakin Syria.

Rasha da China dukkaninsu sun yi Allah waddai da yakin da Amurka ta kaddamar a Kosovo da kuma yakin Libya wanda ya yi sanadiyar mutuwar Kanal Gaddafi, kamar yadda Rasha ta nuna adawa da yakin Iraqi da aka kashe Saddam Hussain.

Alkalumman Majalisar Dinkin Duniya sun ce kimanin mutane sama 100,000 ne suka mutu a rikicin Syria, yayin da kuma dubban mutane suka fice daga kasar zuwa makwabtan kasashe domin tsira da ransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.