Isa ga babban shafi
Syria-MDD

MDD ta nemi dalilin kai wa wakilanta hari a Syria

Wakilan Majalisar Dinkin Duniya sun kai ziyara a yankunan kasar Syria da aka kai harin makamai masu guba bayan an kai wa tawagar hari. Ban Ki-moon yace wakilan sun gana da wadanda harin ya rutsa da su da ke jinya a Asibiti amma ya mika kokensu ga gwamnatin Syria akan harin da aka kai wa tawagar.

Motocin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria
Motocin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria
Talla

A ranar 21 ga watan Agusta ne aka kai wani harin makamai masu guba a Damascus, kuma ‘Yan tawaye sun ce daruruwan mutane ne suka mutu a gabacin Ghauta da Moadamiyet al Sham.

Kungiyar Likitocin masu zaman kansu ta Doctors Without Borders tace kimanin mutane 355 ne suka mutu sakamakon hare haren.

Akan haka ne Majalisar Dinkn Duniya ta aika da wakilai kwararru domin gudanar da sahihin bincike game da al’amarin. Amma akwai hari da wasu ‘Yan bindiga suka kai wa wakilan da safiyar Litinin akan hanyarsu ta zuwa yankin da aka kai haren haren na Makamai masu guba.

A cewar Nesirky Kakakin Majalisar Dinkin Duniya, babu wani rahoton rauni da aka samu bayan an kai wa motar da ke dauke da tawagar hari a yankin Ghauta da ke gabas da Damascus.

Nesirky yace wasu ‘Yan bindiga ne da ba a tantance ba suka bude wa tawagar wuta daga nesa.

Daga kasar korea ta Kudu, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yace wakilan shi sun gana da wadanda hare haren suka rutsa da su da ke jinya a Asibiti.
Gwamnatin Assad da ‘Yan tawaye dukkaninsu suna zargin juna ne akan amfani da makaman masu Guba.

Shugaba Assad ya yi wa Amurka da kwayenta kashedin ga duk wani yunkurinsu na shiga tsakanin rikicin Syria, yayin da Rasha ta yi gargadin rikicin Syria na iya shafar yankin Gabas ta tsakiya idan har Amurka ta abkawa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.