Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Za’a yi binciken makamai masu guba a Syria

Kwamitin tsaro ya bukaci a ba wakilan Majalisar Dinkin Duniya damar tabbatar da zargin Dakarun Assad sun yi amfani da makamai masu guba a wani hari da suka kai a Damascus wanda ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane.

Hoton da wadanda suka shaki guba a hare haren da ake zargin dakarun Assad sun kai a Damascus
Hoton da wadanda suka shaki guba a hare haren da ake zargin dakarun Assad sun kai a Damascus REUTERS/Bassam Khabieh
Talla

‘Yan tawayen Syria sun ce kimanin mutane 1,300 ne suka mutu sakamakon harin, tuni kuma Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah Waddai da harin tare da aikawa da wakilai domin tabbatar da al’amarin.

Bayan fitar da rahoton ne Kwamitin tsaro ya gudanar da wani taron gaggawa, kuma kwamitin ya bukaci a gudanar da kwakkwaran bincike.

"Mambobin kwamitin tsaro sun amince da bukatar Ban Ki-moon na tabbatar da kwakkwaran bincike", a cewar Jan Eliasson Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya.

Wani hoton bidiyo da masu fafutika a Syria suka yada ya nuna wani likita yana kula da yaran da ke cikin mawuyacin hali saboda hare haren da suka ce an kai da makamai masu guba.

Amma Gwamnatin Assad da Rasha sun yi watsi da zargin. Faransa da Amurka da Birtaniya da Korea Ta kudu sun bukaci gwamnatin Assad ta bayar da dama domin wakilan Majalisar Dinkin Duniya su gudanar da bincike

Alkalumman Majalisar Duniya Duniya sun ce sama da mutane 100,000 suka mutu a Syria tun fara zanga-zangar kin jinin gwamnatin Assad a 2011 kuma har yanzu yaki ne ake ci gaba da gwabzawa inda daruruwan mutane suka fice daga kasar zuwa makwabtan kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.