Isa ga babban shafi
Syria-MDD

An fara bincike kan amfani da makamai masu guba a yakin Siriya

A yau litinin ne jami’an Majalisar Dinkin Duniya ke soma gudanar da bincike, kan zargin yin amfani da makamai masu guba kan fararen hula a yakin kasar Syria. Babban Magatakarda na Majalisar Ban Ki-moon ya bukaci jami’an da su mayar da hankali wajen tantance idan har abin da aka yi amfani da shi makami ne mai guba ko kuma a a.Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da manyan kasashen duniya suka ci gaba da tattaunawa kan irin matakin da za su dauka dangane da wannan batu. Ko a jiya an yi doguwar tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaban Amurka Barack Obama da kuma takwaransa na Faransa Francois Hollande dangane da wannan batu, kuma shugabannin sun ce akwai alamun da ke kara tabbatar da cewa sojojin gwamnati ne suka yi amfani da makaman masu guba a kan jama’a,Kwana daya kafin nan kuwa, an yi irin wannan tattaunawar ce tsakanin Obama da kuma David Cameron na Birtaniya, to sai dai har yanzu kasar Rasha na ci gaba da nuna adawarta da daukar wani mataki a kan Syria ba tare da amincewar Majalisar ta Dinkin Duniya ba.Dukkan Bangarorin da ke rikici, wato bangaren Gwamnati da na ‘yan tawayen kasar ta Siriya, suna ci gaba da zargin juna, wajen yin amfani da makaman masu guba, kan fararen hula. 

Wani mutum ya sanya kariya daga makamai masu guba a Siriya
Wani mutum ya sanya kariya daga makamai masu guba a Siriya REUTERS/Bassam Khabieh
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.