Isa ga babban shafi
Syria-MDD

MDD ta nemi a samar da sauyi ta ruwan sanyi a Siriya

Babban Mai shiga tsakani na majalisar dunkin Duniya Lakhdar Brahimi ya bukaci samun chanji na musamman, ta hanyar sauya gwamnati a kasar Syria.Sai dai ‘yan tawayen kasar, sun bayyana cewar batun samar da sabuwar gwamnati ba zai kunshi shugaba Bashar al-Assad da jami’an gwamnatin shi ba.Brahimi ya bayar da wannan sanarwar ne a birnin Damascus, yayin da kasar Rasha, da tafi alakar kud-dakud da Syria ta musanta cewar akwai shirin samarda zaman lafiya, tsakanin Syria da kasar Amurka, wadda ke daya daga cikin masu taimakawa ‘yan tawaye fada da Sojin gwamnatin shugaba Assad.A halin da ake ciki kuma,  Rasha tayi kashedin cewar zai yi wuya a kaucewa mummunan zub-da-Jini, idan aikin mai shiga tsakani na majalisar dunkin Duniya, ya gagara shawo kan fadan da aka kwashe watanni 21 ana tafkawa, da kuma yayi sanadin mutuwar a kalla mutum dubu 45 a kasar.Ministan harkokin wajen Rashan Sergei Lavrov yace, ya zama wajibi ga kasar Amurka da masu hankoron dakatar tashe-tashen hankula a kasar ta Syria, su kara kokari, ganin yadda ake kara fidda tsammanin magance matsalar ta hanyar Diplomasiyya. 

Mai shiga tsakani a rikicin kasar Siriya Lakhdar Brahimi
Mai shiga tsakani a rikicin kasar Siriya Lakhdar Brahimi REUTERS/Khaled al-Hariri
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.