Isa ga babban shafi
Syria-diflomasiya

Rasha ta musanta tayin baiwa Shugaban Siriya mafakar siyasa

Kasar Rasha ta musanta wasu bayanai dake cewa ta tattauna da kasar Amurka domin baiwa Shugaban Siriya Bashar Assad mafaka ta siyasa.Yayinda ake ta shirin sake gagarumin taron kawayen kasar Syria a Paris na kasar Faransa, dake son kawar da Shugaba Bashar al-Assad, kungiyoyin dake sa idanu kan wainar da ake toyawa a Syria sun ce akalla mutane 70 Dakarun kasar suka kashe kafin wayewar gari yau Alhamis.Mukaddashin Ministan harkokin waje na kasar Russia Sergei Ryabkov ya fadi cewa karya ake wa Rasha, don a cewar shi ba ta ce zata baiwa Shugaba Assad mafaka ta Siyasa, bayan kawar dashi ba.Cikin watanni 16 da aka yi ana neman kawar da Shugaban Siriya, bayanai na nuna rayukan mutane da suka salwanta sun haura 16,500.Da fari wasu kafofinn yada labaran Rasha sun yi ta yada labaran dake cewa wasu kasashen duniya karkashin jagorancin Amurka na ta lallashin Hukumomin birnin Moscow domin su baiwa Shugaba Bashar Al-Assad mafakar siyasa.  

Shugaban Siriya Bashar al-Assad
Shugaban Siriya Bashar al-Assad DR
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.