Somalia
Somalia: Al Shabaab ta kafa dokar saka Hijabi
Mayakan kungiyar Al Shabaab a kasar Somalia sun bukaci mata musulmi da ke kasar su tabbatar suna sanya tufafi da ke rufe dukkan jiki, da fuska, ko kuma bulala ta yi aikin akansu, yayin da aka Mayakan suka cafke wasu Matan kusan 100 a garin Buale, mai tazaran kilomita 300 da kudu maso gabashin birnin Mogadishu.
Wallafawa ranar:
Talla
Kodayake rahotanni sun ce an saki matan, amma an gargade su, kada a sake ganinsun cikin shigar banza.
Kungiyar Al Shabaab dai tana rike ne da ikon wasu yankunan kasar Somalia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu