Isa ga babban shafi
Amurka

Rahoto: Syria da Somalia mafi hadari ga ‘Yan Jarida

Hukumar kula da kare hakkin ‘Yan Jaridu a Amurka tace Syria ce kasa mafi hadari ga aikin Jarida a cikin rahoton hukumar na Shekara. An bayyana kasar Iraqi a sahun gaba da Somalia a matsayin ta biyu a jerin kasashen da rayuwar ‘Yan jarida ke fuskantar barazana.

Wata Ma'aikaciyar Jarida a Radiyo Faransa
Wata Ma'aikaciyar Jarida a Radiyo Faransa RFI/Nicolas Falez
Talla

Hukumar tace yawan hare haren da ake kai wa ‘Yan jaridu a Syria babbar barazana ce ga aikin Jarida a cikin kasar.

Amma kasar Iraqi ce kasa ta farko a cikin jerin kasashen da ‘Yan Jarida ke fuskantar barazana.

Tun a 2008 hukumar ta bayyana Iraqi a matsayin ta farko amma rahoton yace a 2012 ba a samu kisan ‘yan Jaridu ba a cikin kasar, sabanin 2013 da aka kashe ‘Yan Jairda 10.

A Somalia, Yan jarida hudu aka kashe a 2013, kuma rahoton hukumar yace yawancin wadanda ake kashewa ‘Yan Jaridar cikin gida ne masu aiki a bangaren Siyasa da cin hanci da rashawa da masu aiko da rahoto a fagen yaki.

Kasar Afghanistan ce a matsayi na 5, Pakistan a matsayi na 9, sai Najeriya da aka bayyana a matsayi na 12.

Jerin kasashe mafi hadari ga ‘Yan Jarida.
1/ Iraq
2/ Somalia
3/ Philippines
4/ Sri Lanka
5/ Syria
6/ Afghanistan
7/ Mexico
8/ Colombia
9/ Pakistan
10/ Russia
11/ Brazil
12/ Nigeria
13/ India

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.