Isa ga babban shafi
Amurka

An kashe ‘Yan Jarida 52 a 2013-Rahoto

Rahoton da wata Kungiyar kare ‘Yan jaridu da ke birnin New York na kasar Amurka Committee to Protect Journalist ta fitar, rahoton yace shekara ta 2013 da ke shirin kawo karshe, na daya daga cikin shekarun da aka fi kashe ‘Yan jaridu a sassa daban daban na duniya.

Laurent Fabius yana jawabi a lokacin bikin juyayin mutuwar 'Yan jaridar RFI Claude Verlon da Ghislaine Dupont da aka kashe a Mali
Laurent Fabius yana jawabi a lokacin bikin juyayin mutuwar 'Yan jaridar RFI Claude Verlon da Ghislaine Dupont da aka kashe a Mali France 24
Talla

Shekarar 2013 ita ce shekara ta biyu da aka fi kashe ‘Yan jarida a duniya tun lokacin da aka fara tara alkalumman kisan na ‘Yan jarida a 1990 a cewar rahoton.

Rahoton ya ce a bana kawai an kashe ‘Yan jarida 52 duk da cewa adadin bai kai na bara ba inda aka kashe ‘Yan jaridu 73 a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.

Rahoton ya ci gaba da cewa kasar Syria ce ke a matsayin kasa ta farko inda aikin jarida ke da matukar hadari, inda a bana aka kashe ma’aikatan yada labarai 21. Akwai kasashe kamar Iraqi da Masar da Somalia da Pakistan da Mali da Brazil da kuma Rasha inda ake kashe masu aikin na yada labarai.

Rahoton yace akwai ‘Yan Jarida kimanin 30 da suka bace a Syria

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.