Isa ga babban shafi
Masar

Masar ta yi wa dokar ta’addanci kwaskwarima akan ‘Yan Jarida

Majalisar Masar ta yi wa kudirin dokar yaki da ta’addanci kwaskwarima, inda aka sauya hukunci dauri akan ‘Yan Jarida zuwa Tara idan har suka wallafa labarin alkalumman hare haren ta’addanci da suka sabawa na gwamnatin kasar.

Shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi
Shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi REUTERS/The Egyptian Presidency/Handout via Reuters
Talla

Rahotanni sun ce majalisar Ministocin kasar sun amince a ci tarar duk wani dan jarida da aka kama ya sabawa gaskiyar labarin haren haren ta’addanci a kasar kudi dala dubu ashirin da biyar zuwa dubu sittin da biyar.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama da suka hada da Kungiyar Amnesty sun soki shirin Gwmanatin Masar na kafa sabuwar doka da ke bayar da damar daure duk wani wanda ya wallafa alkalumman hare haren ta’addanci da suka sabawa na gwamnatin kasar.

A cewar Kungiyar Amnesty sanya wannan doka ya sabawa ka’idar ‘yanci fadin albarkacin baki, tare da tauye hakkin dan adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.