Isa ga babban shafi
Masar

Amnesty ta soki dokar ta’addanci kan ‘yan Jarida a Masar

Kungiyar Amnesty ta soki shirin Gwmanatin Masar na kafa sabuwar doka da ke bayar da damar daure duk wani wanda ya wallafa alkalumman hare haren ta’addanci da suka sabawa na gwamnatin kasar.

Shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi
Shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi REUTERS/Egyptian Presidency/Handout via Reuters
Talla

Ko da ya ke yanzu gwamnatin Masar ta amince ta yi dokar kwaskwarima, da ke barazana ga ‘yan aikin jarida.

A dai cikin watan da ya gabata ne, Gwamnatin Masar ta kafa wannan doka domin kawo karshen yadda ake samun bambancin alkalumma tsakanin na hukumomi da kuma wadanda ‘yan jarida ke bayarwa a duk lokacin aka kai wa jami’an tsaron kasar hari.

Abdel Fatah Al-sisi ya kuduri aniyar murkushe duk wadanda ke neman yi wa gwamnatinsa hawan kawara, da suka hada da ‘yan adawa da kuma ‘yan jaridu.

Sai dai kuma a cewar Kungiyar Amnesty sanya wannan doka ya sabawa ka’idar ‘yanci fadin albarkacin baki, tare da tauye hakkin dan adam.

Dokar dai na iya kara haifar da rashin zaman lafiya a kasar mudin aka yankewa wani wannan hukunci da ya dangance zaman gidan kaso har na tsawon shekaru 2, ga duk wanda ya karya dokar.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba, da kungiyoyin kare hakkin bil’adama ke kalubalantan gwamnatin al-sisi kan tauye hakkin jama’a, tun bayan hambarar da gwamnatin Muhamed Morsi a cikin shekarar 2013.

Sai dai a ko da yaushe Al-Sisi na bayyana cewa gwamnatinsa na daukar matakai ne domin kare Masar daga ayyukan ta’addanci tare da samar da daidaito tsakanin al’umomin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.