Isa ga babban shafi
Burundi

Za a yi taro a Tanzania kan rikicin Burundi

A ranar asabar za a fara wani taro a kasar Tanzania da zai maida hankali kan rikicin kasar Burundi yayin da hankulan kasashen duniya suka karkata kan hanyoyin da za a bi domin kawo karshen zubar da jini da ma tilasta wa Shugaban kasar Pierre Nkuriziza sauya manufarsa ta sake tsayawa takara a wa’adi na uku 

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza REUTERS/Jean Pierre Aime Harerimana
Talla

Ana saran cimma matsaya ta gari tsakanin bangarorin jam’iyyun siyasar kasar Burundi a wannan zaman tattaunawar.

Mahalarta taron na bukatar ceto Burundi daga durkushewa kuma suna hasashen yiyuwar shawo kan Shugaban kasar Pierre Nkuriziza da ya sauya aniyarsa ta neman sake tsayawa takarar shugabancin kasar a wani wa’adi na uku, wanda yin haka ya sabawa kudin tsarin mulkin Burundi.

An gaiyato ilahirin ‘yan siyasar kasar ta Burundi da kungiyoyin fararen fula da shugabanin addinai na kasar da suka hada da musulmai da krista da ma ‘yan ba ruwan mu.

Manzo na musaman daga Majalisar Dinkin Duniya Sa’id Djinnit ya bayana fatarsa ta ganin an cimma nasara da tare da maido da zaman lafiya a kasar ta Burundi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.