Isa ga babban shafi
Ebola

WHO ta fito da sabon tsarin yaki da Ebola

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace ta samo wani sabon tsarin da zai kai ga samun nasarar dakile cutar Ebola a karshen wannan watan na Mayu ne dai hukumar tace zata fara aiki da wannan sabon tsarin.

Jami'an lafiya da ke aikin yaki da Ebola a Liberia
Jami'an lafiya da ke aikin yaki da Ebola a Liberia REUTERS/James Giahyue
Talla

Akwai matakai da dama da hukumar ta ce zata yi amfani da su wajen ganin ta dakile cutar ta Ebola baki daya

Hukumar ta ce lallai Akwai bukatar mayar da hankali, da jajircewa wajen hana yaduwar cutar Ebola zuwa kasashen da ke makwabta da kasashen da cutar ke ci gaba da adabarsu har yanzu.

Sabon tsarin ya kuma kunshi tsofaffin tsare-tsare da hukumar ta gabatar tun a cikin watan Agusta bara, a lokacin da cutar ke ta addaba mutanen, musamma a kasashen Guinea da Liberia da kuma Saliyo.

Liberia da ke daya daga cikin kasashen da cutar Ebola ta fi kamari, ta bayyana cewar tun a cikin watan Maris da ya gabata, rabon ta da a samu wani da ya kamu da cutar, sai dai WHO ta yi gargadi cewar hakan ba yana nufin babu cutar a kasar kwata-kwata ba.

Sabbin alkalluman hukumar dai na cewa sama da mutane dubu 26 ne suka kamu da cutar Ebola yayin da cutar ta kashe sama da mutane dubu 10.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.