Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Zidane da Ronaldo sun jagoranci wasan Ebola

Tsoffin ‘yan wasan kwallon duniya Zinedine Zidane da Ronaldo na Brazil sun jagoranci wani wasan yaki da Talauci karo na 12 a jiya Litinin a filin wasa na kungiyar Saint-Etienne a Faransa. An gudanar da wasan ne na musamman domin yaki da cutar Ebola tare da samar da kudaden tallafi ga kasashen yammacin Afrika guda uku inda cutar ta fi yin kisa.

Tsoffin 'yan wasan Faransa Zinedine Zidane da Thierry Henry
Tsoffin 'yan wasan Faransa Zinedine Zidane da Thierry Henry REUTERS
Talla

Zidane daRonaldo jekadu ne na musamman ga hukumar samar da ayyukan ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya.

Daga cikin tsoffin ‘yan wasan da suka rufe wa su Zidane da Ronaldo baya akwai, Fabien Barthez da Eric Abidal da Clarence Seedorf da David Trezeguet da Jay-Jay Okocha na Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.