AU ta bukaci Congo ta bayar da dama a yaki ‘Yan tawayen Rwanda
Kungiyar Kasashen Afirka ta AU ta bukaci Jamhuriyar Demokradiyar Congo ta bai wa dakarun Majalisar Dinkin Duniya damar taka rawa don fatattakar ‘yan tawayen Rwanda, bayan rashin jituwar da aka samu sakamakon zargin hafsoshin sojin kasar da cin zarafin Bil Adama. Shugaba Joseph Kabila ya yi watsi da bukatar Majalisar na hukunta hafsoshin sojin biyu ko kuma Majalisar ta cire hannunta a yakin.
Wallafawa ranar:
Boubacar Diarra, wakilin Afirka ta Gabas a taron Majalisar tsaro ta kungiyar kasashen Afirka ya ce bukatarsu shi ne ganin an hada karfi da karfe tsakanin sojojin Congo da na Majalisar domin murkushe yan tawayen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu