Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya tace Somalia na fuskantar matsalar yunwa

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Kin Moon, ya yi gargadin cewa Somalia na gab da fadawa cikin yunwa muddun ba a kai doki zuwa kasar cikin gaggawa ba. A jiya Laraba ne Ban Kin Moon ya sanar da hakan bayan ya gana da shugaban kasar Hassan Sheikh Mahmoud, a yayin ziyarar daya kai birnin Mogadishu, inda yace al’ummar Somalia sama da miliyan uku ne ke bukatar taimako.Don haka Ban ya yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta tallafawa kasar, domin kaucewa halin da kasar ta taba fadawa a baya na matsanancin yunwa.Wani rahoto na majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa yanzu haka, yara sama da dubu 200 ke rayuwa cikin karancin abinci, inda majalisar ta kara da cewa tana bukatar kudi akalla Dalar Amurka miliyan 933 sabanin dala miliyan 318 da ta samu a matsayin tallafin da ta samu, don kai dauki. kasar Somalia dai na cigaba da fuskantar matsalolin tsaro sakamakon ayyukan kungiyar al-Shababa mai alaka da kungiyar nan ta al-Qaida, lamarin daya haddasa asarar rayukan mutane da dama da kuma salwata dukiya a wannan kasa, da a baya ta rasa rayukan mutane sama da dubu 250 yawancin su kuwa yara kanana, sakamakon matsananciyar yunwa.  

Wani yaro dake fama da matsalar yunwa a kasar Somalia
Wani yaro dake fama da matsalar yunwa a kasar Somalia
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.