Isa ga babban shafi
Somalia

Mutane 260,000 suka mutu a Somalia sanadiyar fari

Wani sakamakon binciken Majalisar Dinkin Duniya ya gano cewa kusan mutane 260, 000 suka mutu sakamakon farin da ya afka wa kasar Somalia daga shekarar 2010 zuwa 2012.

Wata Uwa dauke da danta da Fari ke neman halakawa a  kasar Somalia
Wata Uwa dauke da danta da Fari ke neman halakawa a kasar Somalia Reuters/Feisal Omar
Talla

Rahoton, da hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa rabin wadanda farin ya rutsa da su yara ne kanana, ‘yan kasa da shekaru biyar.

Alkaluman sun nuna cewa mutanen da suka mutu sun haura 220,000 da suka mutu, lokacin farin da aka yi a kasar a shekarar 1992.

Tsananin karancin ruwa ne ya haddasa matsalar, kuma yakin da ake yi, tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen ma su dauke da makamai, ya sa lamarin ya tabarbare.

A watan Yulin shekarar 2011, Majalisar Dinkin Duniya ta fara ayyana matsalar fari a yankin kudancin Bakool da lardin Shabelle, da ke hannun mayakan, masu tsananin kishin Islama na kungiyar Al-Shabab, da ke da alaka da al-Qaeda.

Sai dai kungiyar al Shabab ta karyata cewa akwai fari a kasar, inda ta hana kungiyoyin bayar da agaji na duniya kai tallafi zuwa wadannan yankunan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.