Isa ga babban shafi
Somaliya

MDD Ta ayyana annobar yunwa a kasar Somaliya

Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana cewa akwai tsananin yunwa a wasu yankunan Kudancin kasar Somaliya. Majalisar ta kuma yi gargadin cewa in dai har ba a dauki kwararan matakan gaggawa ba, lamarin zai iya tsawaita har zuwa watanni 2 masu zuwa, a kasar da yaki ya daidaita a yankin kahon nahiyar Africa. Jami’in majalisar mai kula da agajin gaggawa a kasar ta somaliya, Mark Bowden yace yunwa da ba a ga irin ta ba cikin shekaru 20 ta riga ta far ma yankunan kudancin Bakool da kudancin Shabelle, kuma dole a dau matakan gaggawa.Suma kasashe Kenya da Ethiopia suna fuskantar irin wannan barazanar.Yankin na hannun Kungiyar Musulmi masu dauke da makamai ta Al Shabaab, da ke da alaka da kungiyar Al Qaeda ne.A farkon wannnan watan kungiyar ta Al Shabaab ta dage takunkumin da ta sa kan shigar da abinci yankin, inda a baya tace yana sa jama’ar yankin na dogaro kan taimako daga kasashen waje. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.