Isa ga babban shafi
Sudan

An saki Ma’aikatan agaji da aka sace a Darfur

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace an saki wasu ma’aikatan kungiyoyin agaji guda uku da aka sace tsawon kwanaki 32 a yankin Darfur a kasar sudan. A Cikin wata Sanarwr, rundunar wanzar da tsaron tace ma’aikatan da aka sace, Mustafa Abdalla Adarge da Mohamed Abu Elgassem da Ahmed Elsayed, dukkaninsu an sake su kuma suna cikin koshin lafiya.

Sojojin Wanzar da tsaro a yankin Darfur
Sojojin Wanzar da tsaro a yankin Darfur Reuters
Talla

A ranar 20 ga watan Yuni ne wata kungiyar agaji ta Goal ta tabbatar da cewa wasu ‘Yan bindiga sun sace Jami’inta a lokacin da ya ke tukin motarsa a kusa da garin Kutum.

Zuwa yanzu dai babu wani bayani akan ‘Yan bindigar da suka sace mutanen guda uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.