Isa ga babban shafi
Sudan

Sudan na nazarin yin amfani da karfin Soji a Darfur

Shugaban yankin mulkin Darfur na kasar Sudan ya bukaci yin amfani da karfin soja wajen murkushe mayaka ‘yan tawaye na kabilu da ke yankin na Darfur, ganin yadda lamarin ke kara ta’azzara.

Al-Tigani al-Sessi, Shugaban da ke kula da ion yankin Darfur
Al-Tigani al-Sessi, Shugaban da ke kula da ion yankin Darfur Reuters
Talla

Eltigani Sessi ya fadawa taron kwanaki 2 na jakadun kasar Sudan, a birnin El-Fasher da ke Jihar Arewacin Sudan cewa matakin Soja ya zama dole domin dukkan matakan sulhu da aka sani na gargajiya an bi amma rikicin sai karuwa ya ke yi.

Yace ya zama wajibi Dakarun kasar su shiga cikin rikicin kabilancin domin kawo karshen sa.

A bana kawai, rikicin kabilanci, daya hada da ‘yan tawaye da ke yakar Gwamnati, sun tilastawa mutane sama da 300 tserewa daga yankin na Darfur, alkalumma da suka zarce na shekaru biyu da suka gabata a jere.

Jakadun na gudanar da taron ne duk bayan shekaru biyu, domin nazarin lamurra a yankin Darfur, inda rikicin kabilanci ya ki ci ya ki cinyewa sama da shekaru 10.

Eltigani Seisi wanda ya ke jagorantar kwamiti na musamman da ke aiwatar da tsarin zaman lafiya a yankin, ya fadawa taron cewa sun tsara yadda za su kwace makamai daga hannun ‘yan tawaye da mayaka na kabilu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.