Isa ga babban shafi
Amurka-Africa

John Kerry ya fara ziyara a nahiyar Africa

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry da yanzu haka ke gudanar da ziyarar aiki a Africa ya yi gargadin cewar dole a kawo karshen rikicin kasar Sudan ta Kudu.John kerry ya fara yada zango ne a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia, kasar da ake gudanar da zaman tattaunwara rikicin kasar ta Sudan Ta kudu.Bayan ganawa da sauran wakilan kasashen Ethiopia da na Kenya da kuma Uganda akan rikicin kasar ta Sudan ta kudu a yau alkhamis, kerry yace ya tabbatar kowa ya amince bisa yarjejeniyar kawo karshen rikicin kasar domin kaucewa fadawa yakin basasa.Ya kuma bayyana goyon bayan Amurka na tunkarar hanyoyin warware rikice rikicen a nahiyar Africa. A cigaba da ziyarar dai batun rikice rikicen kasashen Afrika ta Tsakiya, Somalia da kuma Jamhuriyar Demokradiyar Kongo su zasu mamaye tattaunawar da za a yi, kuma wani na hannun damanshi ya ce Kerry zai yi jawabi, da jan hankali ga bangarorin dake rikici da juna su sasanta.Amurka dai ta taka gagarumar rawa wajen taimakawa kasar sudan ta kudu samun yanci kai a shekara ta 2011.Yanzu haka fada tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da kuma tilastawa sama da miliyan tserewa daga gidajensu.  

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry
Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry REUTERS/Larry Downing
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.