Isa ga babban shafi
Faransa-Masar

Shugaban Faransa Hollande na ziyara a Tunisiya

Shugaban Faransa, Francois Hollande da ke ziyara a kasar Tunisia, ya bayyana goyon bayan shi kan yadda hukumomin kasar Tunisia ke gudanar da mulkin kasar, tare da kiran a tabbatar da dawo da mulkin democradiyya a kasar Masar. Shugaba Hollande, ya shaida wa manema labaru cewa akwai matsala in har aka hambarar da wani zababben shugaba.Kasar Tunisiya ma, da ke karkashin jagorancin jama’iyyar masu kishin Islama ta Ennahda, mai alaka da ta ‘yan uwa musulmi ta kasar Masar, ta yi fama da matsaloli da dama a ‘yan watannin da suka gabata.Shugaban kasar ta Tunisiya Moncef Marzouki, da ya amince cewa akwai banbanci ra’ayi a tsakanin jama’iyyar masu kishin islama mai mulkin kasar, da bangaren adawa, ya kawar da yiwuwar samun juyin mulki kamar yadda aka gani a kasar ta Masar.Ziyarar kwanaki 2 ta shugaba Hollande, ita ce ta farko da wani shugaban Faransa ya kai Tunisia, tun bayan, da aka kifar da gwamnatin dan kama karya, kuma tsohon aminin kasar ta Faransa, Zine El Abidine Ben Ali, a watan junairun shekarar 2011, lamarin da ya haifar da juyin juya halin kasashen larabawa.Ana sa ran shugaba Hollande zai bayar da sanarwar ci gaba da baiwa Tunisia tallafi daga Faransa, da a halin yanzu ya kai YURO miliyon 500. 

Shugaban Faransa Francois Hollande da shugaban kasar Tunisiya Moncef Marzouki a birnin Tunis
Shugaban Faransa Francois Hollande da shugaban kasar Tunisiya Moncef Marzouki a birnin Tunis REUTERS/Anis Mili
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.