Isa ga babban shafi
Ukraine

Jami'an kasashen Turai za su kai ziyara Ukraine

A yau Alhamis ministocin harkokin wajen kasashen Hungary, Slovakia da kuma na Czech zasu kai wata ziyarar aiki a kasar Ukraine, domin ganawa da jami’an sabuwar gwamnatin da aka kafa, bayan hanmabrar da Victor Yanukovich a makon da ya gabata. Wannan ziyarar da ministocin uku zasu kai dai ta biyo bayan yunkurin da kasashen duniya masu karfin tattalin arziki ke tayi ne, wajen ganin a kwantar da tashin hankalin da kasar ta Ukraine ke fama da shi, tare da taimakawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar, bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar, Victor Yanukovich sakamakon zanga zangar kin jinin gwamnatinsa da ta janyo asarar rayukan mutane sama da tamanin.A baya wasu wakilan kasashen Turai sun kai ziyara kasar a yayin da kungiyar Tarrayar Turai ta yi alkawarin taimakawa kasar da kudi, domin ceto ta daga matsalar tattalin arzikin data fada.Manyan muradun kasashen dai a wannan ziyara ita ce ganin kasar ta Ukraine ta sanya hannun a yarjejeniya hadin guiwa da kungiyar tarrayar Turai a cikin kankanin lokaci, batun da shine ya haifar da rikicin kasar wace har ta kai ga hanbarar da gwamnatin kasar.  

Shugaban Rikon kasar Ukraine, Oleksander Turchinov
Shugaban Rikon kasar Ukraine, Oleksander Turchinov
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.