Isa ga babban shafi
Ukraine

'Yan sanda sun yi wa masu zanga zanga dirar mikiya a Ukraine

Al’amura na cigaba da ritsabewa a Ukraine inda ‘yan sanda suka yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga-zanga a Kiev dake Babban Birni Kasar. Rahotani na bayyana cewa an samu mutuwar mutane uku sakamakon dirar mikiyar.‘Yan sandan sun tarwatsa masu zanga-zanga da suka yi zaman durshan a harabar ofisoshin babban birni kasar Kiev.Yayin wanan arrangama ‘yan sandan su yi amfani da barkono mai sa hawaye da harshashin roba don murkushe ‘yan adawan.Wanna na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban kasa Viktor Ianoukovich yayi kira ga ‘yan kasar da su kaucewa shiga wanan tarnakin, da kan iya tsuduma kasar cikin rudani,A halin da ake ciki kuma, kwamishinar harakokin wajen kungiyar tarayyar Turai, Catherine Aston ta bayyana damuwar ta kan yadda al’amura ke gudana a Ukraine.Ya zuwa yanzu bangarorin biyu, ‘yan sanda da masu zanga-zanga na ciggaba da bawa hamuta iska a wasu sassa na birnin Kiev. Daya daga cikin masu zanga-zangar yace za su cigaba da takawa gwamnatin shugaba Ianoukovich burkin har sai sun samu biyan bukata. 

'Yan sanda sun far wa wani dan adawa a Ukraine
'Yan sanda sun far wa wani dan adawa a Ukraine REUTERS/Vasily Fedosenko
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.