Isa ga babban shafi
Ukraine

Shugaban kasar Ukraine ya amince ya yi murabus

Yau asabar, Wani dan majalisar dokokin kasar yukrain yace shugaba Viktor Yanukovych ya amince ya yada kwallon magoron don ya huta da kuda. Dan majalisar mai suna Mykola Katerynchuk, na bangaren jama’iyyar Batkivshchyna mai adawa, ya shaida wa manema labaru cewa shugaba Yanukovych ya amince da yin murabus ne, yayin ganawar shi da jamgoran masu zanga zangar Arseniy Yatsenyuk.Wannan na zuwa ne yayin da rikin kasar ke ci gaba da kazanta, inda kusan mutane 100 suka mutu, yayin zanga zangar neman kifar da gwamnati.Watakila wannan matakin da shugaban ya dauka, ya kawo karshen zanga zangar da aka shafe watanni ana yi. 

Shugaban kasar Ukraine Viktor Yanukovych  yana ganawa da manema labaru a birnin Kiev
Shugaban kasar Ukraine Viktor Yanukovych yana ganawa da manema labaru a birnin Kiev Reuters/Mykhailo Markiv/Ukrainian Presidential Press Service
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.