Isa ga babban shafi
DRC Congo

‘Yan tawayen jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun mika Wuya

‘Yan Tawayen Janhuriyar Demokradiyar Congo sun sanar da mika Wuya tare da ajiye makaman su, sakamakon nasarar da Dakarun gwamnatin kasar dake samun goyan bayan Sojin Majalisar Dinkin Duniya suka samu akansu.

'Yan tawayen M23 a Congo
'Yan tawayen M23 a Congo
Talla

Kungiyar ta M23 dai ta sanar da cewar ta kawo karshen tawayen da ta ke yi ne, kuma yanzu za ta kama hanyar tattaunawa dan cimma muradunta.

Kwamandan sojin kasar Jean-Lucien Bahuma ya ce nasarar da suka samu, za ta ba su damar aiwatar da Doka da Oda.

“Yace yanzu za mu samu damar aiwatar da Doka da Oda a cikin kasa, domin ‘yan tawayen M23 sun kafa wata gwamnati ce a wannan wuri na Yurigogo da Rushturu, kuma wannan ya zo karshe. Baya ga haka kuma wannan gagarumar nasara ce a gare mu”

Kasar Amurka dai ta ji dadin mika Wuyan da ‘yan tawayen suka yi, ta kuma yi kira akan gaggauta shimfida batun tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, domin kai karshen tawaye a kasar ta Congo mai dimbin Arziki.

Dakarun hadin Guiwa na majalisar dunkin Duniya da jamhuriyar Dimokradiyyar Congo dai sun kaddamar da farmaki ne a ran 25 ga Watan Ocotoba, abin da yayi sanadin tura ‘yan tawayen zuwa wani wuri mai nisan Kilomita Tamanin 80 Arewacin garin Goma, kusa da kan iyakar Kasar da Kasar Rwanda.

Dama dai Jami’an Majalisar dunkin Duniya da na Gwamnatin Kinshasa, sun yi ta fito da zargin Kasar Rwanda da taimakawa ‘yan tawayen harma takan aika Dakarun ta zuwa fagen fafatawa da ‘yan tawayen ke yi da Sojin Gwamnati, sai dai hukumomi a Kigali na ci gaba da musanta wannan zargi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.