Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta nemi a dakatar da hukuncin kisa a Najeriya

Kungiyar kare hakkin dan adam ta duniya, Amnesty International, tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyin 8, sun yi kira ga hukumomin Najeriya su dakatar da zartar da hukuncin kisa kan fursononin da aka yanke musu hukuncin.

Gwamnan Jahar Edo Adam Oshiomhole
Gwamnan Jahar Edo Adam Oshiomhole globalnews
Talla

Kungiyoyin sun yi kira ga hukumomi a kasar su fara aiwatar da yarjejeniyar da kasashen Duniya suka amince kan dakatar da aiwatar da hukuncin.

Kungiyoyin sun nuna damuwar su kan halin rashin tabbas da Thankgod Ebhos ke ciki, bayan da ya tsallake rijiya da baya a lokacin da aka kusa rataye shi tare da wasu mutanen 4, a gidan yarin garin Benin a Jihar Edo.

Sanarwar da kungiyar ta Amnesty ta fitar, tace wasu rahotanni na danganta hukumomi a Jihar ta Edo da shirin neman wata kotu, ta canza yadda za a aiwatar wa mutumin hukuncin, daga harbi zuwa rataya, tare da nemen hukumomin gidan yarin na Benin su mayar da shi Kaduna, inda aka yanke mishi hukuncin.

Kungiyoyin sun yi Allah wadai da aiwatar da hukuncin kisan Chima Ejiofor da Daniel Nsofor da Osarenmwinda Aiguokhan da Richard Igagu a ranar 24 ga watan Yunin wannan shekarar, ba tare da bin doka ko sanar da iyalan su ba.

A lokacin Thankgod Ebhos ya kai labari ne bayan zuwa gaban hauni, saboda hukuminin gidan yarin sun gano cewa na shi hukucin na bukatar harbi ne.

Yanzu haka kungiyoyin 8, suka nemi hukumomi a Najeriya, su gaggauta dakatar da aiwatar da hukuncin na Kisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.