Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba'a binciken kashe-kashen da 'Yan sanda ke yi a Najeriya- Amnesty

Kungiyar dake kare hakkin Bil adama ta Amnesty International, ta zargi rundunar ‘Yan sandan Najeria da rashin gudanar da bincike kan ‘Yan sandanta da ake zargi da harbe mutane da dama bada alhakinsu ba.

'Yan sandan Najeriya
'Yan sandan Najeriya
Talla

A wani rahoto da kungiyar ta fitar, ta yi ikrarin cewa a mafi yawan lokuta ba a yiwa iyalan wadanda abin ya shafa bayani kwakwakkara, inda rahoton ya gudanar da binciken tun daga shekarar 2009.

“Koda yake akwai wasu ‘yan sandan da aka gurfanar a Najeriyar, amma da dama ba a yi hakan ba.” Rahotan ya bayyana.

Sai dai a daya bangaren, mai Magana da yawun rundunar ‘Yan sandan ta Najeriya, Mike Mba, ya gayawa Kamfanin Dillancin labarai na AFP, cewa bai ga rahoton ba saboda haka ba zai mayar da maratani akai ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.