Isa ga babban shafi
Najeriya

Sarkin Musulmin Najeriya ya shawarci gwamnati ta amince da sanarwar Boko Haram

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na III ya shawarci gwamnatin tarayyar Najeriya akan ta amince da sanarwar dakatar da buda Wuta da kungiyar Ahlussunnah lidda'awati wal-jihad da aka fi sani da Boko Haram ta bayar, domin ceto Najeriya daga matsalar tsaro da ta ke fama da shi.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar na III yana gaisawa da shugaba Goodluck Jonathan
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar na III yana gaisawa da shugaba Goodluck Jonathan
Talla

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya fadi haka ne  a lokacin da ya ke karbar bakuncin babban Hafsan Sojin Najeriya Laftanal Janar Azubueke Ehijireka, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa.

Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III ya ce a lokacin da suka ji tayin tsagaita buda Wutar da kungiyar  Boko Haram ta bayyana, sun yi maraba da shi.

Ya ce wannan al’amari ne da ya kamata mu sanar da gwamnatin tarayya, cewar ya kamata ta yi na’am da shi, ba wai kawai ta ce bangaren kungiyar ne ya sanar da tsagaita buda Wuta ba, dan haka ba za ta kula wannan sanarwa ba.

Mai Alfarma yace sunga ya dace su shawarci gwamnatin tarayya cewar ya kamata ta duba wannan zance domin ai ta hanyar bangaren ne za’a iya kai ga Uwar kungiyar in har bangaren ne yake Magana.

Don haka ba batu ne na yasuwa ba, domin ai mutane sun san ‘ya’yan kungiyar, koda gwamnati bata sansu ba, dan haka a karbi tayin su, a zanta dasu aji bukatun su, daga nan za’a samar da zaman lafiya ga kasa.

Mai Alfarma haka ma yayi kira ga masu hankoron gangamin raba Najeriya dasu daina saboda ba batu ne mai muhimmanci bag a daukacin al’ummar kasar.

Shima dai a nasa jawabin babban Hafsan Sojin kasar Leutenal General Azubueke Ehijireka Yace lokacin da yaji mutane na batun raba Najeriya, ya kira wani Abokin sa, yace masu wannan tunanin su fara tunanin kashe daukacin Sojin kasar, don muddin Sojin Najeriya na a raye wannan batun ba mai yiyuwa bane.

Yace hadin kan Najeriya ba abinda za’ayi wasa dashi ban, ba kuma abinmda za’a zauna ayi muhawara dashi bane, dan haka Sojin Najeriya zasu kara zage-Damtse domin tabbatar da hadin kan kasa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.